Wasanni

Man City ta kawar da Real Madrid daga gasar zakarun Turai

Manchester City ta doke Real Madrid da ci 2-1 a karawar da suka yin a cin kofin zakarun nahiyar Turai abinda ya bata nasara zuwa mataki na gaba.

Magoya bayan kungiyar Manchester City yan lokuta bayan samun nasara
Magoya bayan kungiyar Manchester City yan lokuta bayan samun nasara Reuters
Talla

Wannan nasara ta baiwa City damar fitar da Real Madrid daga gasar gaba daya da ci 4-2 domin zuwa matakin kusa da na kusa da na karshe.

Mai horar da ‘Yan wasan City Pep Guardiola wanda ya bayyana farin cikin sa da nasarar, yace lokaci yayi da zasu sake zage damtse domin lashe kofin a karon farko.

Jadawalin wasa na gaba ya nuna cewar Manchester City zata kara da Olympique Lyon ta kasar Faransa wadda ta fitar da Juventus a karawar da suka yi.

Juventus ta doke Lyon da ci 2-1 bayan Cristiano Ronaldo ya jefa kwallaye biyu a raga, amma kuma da aka tara da kwallo guda da Lyon ta jefa a ragar Juventus a karawar farko da akayi, sai alkaluma suka tashi 2-2, amma Lyon ta samu nasara saboda kwallo guda da ta jefa a raga a gidan Juventus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI