'Yan sandan Uganda sun tarwatsa magoya bayan Bobi Wine

Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine
Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine REUTERS/James Akena/File Photo

Fitaccen mawakin Uganda kuma dan takarar shugaban kasa Bobi Wine, yace 'Yan Sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashi wajen tarwatsa magoya bayan sa dake halartar gangami a Gabashin kasar.

Talla

Wine mai shekaru 34 yace ya tafi garin Mbale dake Gabashin Uganda domin halartar wani shirin rediyo amma Yan Sanda da soji suka haan shi isa, yayin da suka tarwatsa magoya bayan sa wajen amfani da harsashin roba da hayaki mai sa hawaye.

Rahotanni sun ce Bobi Wine na cigaba da samun goyan bayan ganin yadda wasu al’ummar kasar suka gaji da jagorancin shugaba Yoweri Museveni wanda ya kwashe dogon lokaci yana jagorancin kasar, yayin da ake zargin sa da cin hanci da rashawa da kama karya da kuma cin zarafin Bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI