Ya zama wajibi mazauna Paris su sanya kyallen dake rufe baki da hanci
Wallafawa ranar:
Yan Sanda a Faransa sun ce daga gobe ranar litinin ya zama wajibi mazauna birnin Paris babban birnin kasar su sanya kyallen dake rufe baki da hanci ko kuma takunkumi domin kare kan su daga kamuwa da cutar corona.
Sanarwar da rundunar yan Sandan ta gabatar jiya asabar tace daga karfe 8 na safiyar litinin ana bukatar masu shekaru 11 zuwa sama suyi amfani da kyallen a wuraren dake dauke da jama’a da dama.
Yan Sandan sun ce bincike ya nuna musu cewar tun daga tsakiyar watan jiya cutar corona na yaduwa a cikin jama’a a Yankin, wanda ke nuna cewar akalla mutane 400 ke kamuwa da ita kowacce rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu