Afrika

Yan adawa na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga a Mali

Ibrahim Boubacar Keita ,Shugaban kasar Mali
Ibrahim Boubacar Keita ,Shugaban kasar Mali REUTERS/Michele Tantussi

Yan Siyasa tareda hadin gwiwar kungiyoyin farraren hula a Mali sun sanar da shirin sake gudanar da zanga-zangar tilstawa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita sauka daga kujerar shugabancin kasar ranar 11 ga wannan watan .

Talla

Daya daga cikin masu magana da yahun hadakar kungiyoyin siyasa na kasar Choguel Maiga, ya na mai cewa a ranar talata ba za su janyewa ba, har sai hakar su ta cimma ruwa ,musaman saukar shugaban kasar daga madafan ikon kasar ta Mali.

Shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita na samun goyan bayan kasashe, sai dai hakan ba zai hana yan siyasa da kungiyoyin farraren hula dake kalon sa a matsayin wanda ya gaza neman ya sauka daga matsayin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.