Kasuwar Bera ta kankama a Arewacin Kamaru
Wallafawa ranar:
A Guidiguis, gari dake karkashin karamar hukumar Mayo-Kani na lardin arewa mai nisan kasar Kamaru, Bera na daya daga cikin kayan abinci mai muhimmaci bisa al’ada ga kabilun yankin da suka hada da Mufou da Toupouri.
To sai dai a baya –bayan nan lamarin ya zarta tunanin sauran jihohin kasar, inda ake auna Berayen a mudu a a akasarin kananan kasuwannin garin na Guidiguis, inda ake saida Mudu daya dake daukar akalla kankanan Bereye 5, kan kudin kasar Cefa 200.
Wannan lamari dai har ya sanya masu yawon bude ido ziyartan kasuwannin yankin domin baiwa idanunsu abinci.
Wani hoton bidiyo dake yawo a kafar intanet yanzu haka ya bayyana yadda al’ummar garin ke kama Berayen da kuma muhimmacinsu a garasu.
Bisa al'ada dai a kasashen Asia musamman China aka saba ganin masu cin Beraye, amma abin mamaki sai gashi, ashe a kasar Kamaru ma akwai masu wannan al'ada ko sha'awa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu