Nijar-Faransa

Sojin Nijar sun fara farautar wadanda suka kashe masu yawon bude ido

Sojin Nijar a sansanin Bosso, 16 ga watan Yuni, 2017
Sojin Nijar a sansanin Bosso, 16 ga watan Yuni, 2017 ISSOUF SANOGO / AFP

Dakarun Nijar tare da goyon bayan sojin saman Faransa sun kaddamar da farautar maharan da ake zargi da kisan mutane 8 ciki har da Faransawa 6, yayin da masu gabatar da kara a Paris suka sanar da shirinsu na gudanar da bincike a kan wannan aika aika.

Talla

Rundunar sojin Faransa wacce ke da dakaru dubu 5 da dari 1 da ke yaki da ta’addanci a yankin Sahel, ta ce za ta samar da gudummawa ta sama don wannan gagarumin aikin farauto wadanda suka yi wannan aika aika.

Faransawa ‘yan yawon bude ido 6, tare da mai yi musu jagora da direban motar da suke ciki ne wasu ‘yan bindiga a bisa babura suka kashe a lahadin da ta gabata, a kusa da garin Koure, a wani gandun dajin dabbobi.

Jamhuriyar Nijar na fama da matsaloli da suka hada ta ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a kudancin kasar daga Najeriya, da kuma yammacin kasar daga Mali.

A wata sanarwa a birnin Paris, masu binciken kan abin da ya shafi ayyukan ta’addanci sun ce za su binciki zarge zargen kisan kai da ake yi wa kungiyar ‘yan ta’adda masu aikata laifuka.

Wannan ne karo na farko da aka kai wa Turawan yamma hari a yammacin jamhuriyar Nijar, wanda ya bunkasa sakamakon ziyarar da masu yawon bude ido suke kaiwa, tun shekaru 20 da suka wuce, saboda kasancewar wasu na’ukan rakuman daji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI