Bakonmu a Yau

Bikin 'yancin kan Chadi: An baiwa Deby mukamin Marshall

Sauti 03:45
An karrama Idris Deby da mukamin Marshall
An karrama Idris Deby da mukamin Marshall AFP/Renaud MASBEYE BOYBEYE

A Talatar nan, al’ummar Chadi suka gudanar da bukukuwan cika shekaru 60 da samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallakar Faransa.Sai dai bikin na bana ya sha bamban da na shekarun da suka gabata, domin kuwa an yi amfani da wannan rana wajen bai wa shugaban kasar, Idris Deby Itno mukamin Marshall, sakamakon rawar da ya taka don samar wa kasar ci gaba.Sarkin Hausawa N’djamena Mai Martaba Alhaji Mustapha Ibrahim Ahmad, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal muhimmancin wannan rana ga al’ummar kasar ta Chadi.