An karrama Idriss Deby da mukamin Marshall
Rundunar Sojin Chadi ta yi bikin karrama shugaban kasa Idris Deby Itno da mukamin Marshall, a daidai lokacin da kasar ke bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa.
Wallafawa ranar:
Majalisar Dokokin kasar ta amince da baiwa shugaba Deby wannan mukami bayan da ya jagoranci dakarun Chadi wajen fatattakar mayakan Boko Haram da ke yankin Tafkin Chadi a watan Afrilu.
Shugaban Majalisar dokokin kasar Haroun Kabadi ya bayyana Deby a matsayin wani madubin kasar, inda ya shaida masa cewar har yanzu Chadi na fuskantar barazanar kungiyar Boko Haram da ayyukan 'yan ta’adda.
Yayin bikin na Talata, shugaba Idris Deby ya saki firsinoni 538, cikin su har da Janar Abdelkader Baba Ladde, wani tsohon dan tawayen kasar da yayi yaki daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
A watan Disamban bara wata kotu ta yanke wa Janar Ladde hukuncin daurin shekaru 8 a gidan yari saboda samun sa da laifin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da fyade da kuma kona gidaje.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu