Najeriya

Najeriya:Mun fatattaki 'yan Boko Haram daga arewa maso gabas - Buratai

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai. Pulse.ng

Babban hafsan sojin Najeriya , Tukur Buratai, ya ce daakarun kasar sun fatattaki mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, inda yanzu a jihar Borno kawai suka saura.

Talla

Buratai, wanda ke daya daga cikin manyan hafsoshin tsaron kasar da al’umma ke kiraye kirayen su yi murabus ko kuma a tsige su, ya ce rundunar sojin kasar na tattara bayanan sirri da zummar fatattakar mayakan Boko Haram daga jihar Borno gaba daya.

Wata sanarwa daga fadar shugaban Najeriya, wacce ta samu sa hannun kakakin fadar, Garba Shehu ta jaddada ikirarin da Buratai ya yi, inda ta ce a taron da yayi da shugaba Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka.

Sai dai yayin da Buratai ke wannan ikirari, a baya bayan nan ma sai da aka samu matsalar hare haren ‘yan Boko Haram a makwafciyar jihar Borno, wato Yobe, inda mayakan Boko Haram din suka farmaki garin Dapchi a watan Mayu da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI