Najeriya

'Yan ta'adda ba su fi dakarun Najeriya makamai ba - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kamala taron tsaron kasa da ya yi da wasu gwamnonin kasar, inda ya sake jaddada muhimmancin kare fararen hula da kuma kawo karshen tashe tashen hankulan da suka addabi kasar.

Talla

Buhari ya bukaci inganta dangantaka tsakanin jami’an tsaro da al’ummomin da suke aiki a cikin su, musamman wajen musayar bayanan asiri, yayin da ya bukaci kwamandojin tsaro da jagorancin yaki da batagari da su tabbatar da kare lafiyar fararen hular.

Taron majalisar tsaron ya kuma amince da rawar da talauci da rashin aikin yi ke takawa wajen ruruta matsalar tsaron a fadin Najeriya, inda ya bukaci hadin kai a matakai daban daban domin shawo kan matsalar.

Buhari yayi amfani da taron wajen watsi da ikrarin cewar Yan ta’addan dake Yankin Arewa Maso Gabas sun fi dakarun Najeriya makamai da kudade, inda yake cewa yanzu haka Yan ta’addan farautar abinci suke yi wajen kai hari kasuwanni da gidajen jama’a domin samun abinda za su ci.

Shugaban kasar ya sake kalubalantar hafsoshin tsaron kasa wajen musayar bayanai da kuma aiki tare domin ganin an kawo karshen wadannan matsaloli da suka addabi Najeriya.

Shugaban Gwamnoni Kayode Fayemi da Gwamnan Borno Babagana Zulum sun bayyana matsalar da ake samu tsakanin hafsoshin tsaron kasa a matsayin babbar matsalar dake yiwa yakin zagon kasa, yayin da suka bukaci shugaban ya duba yadda zai taimakawa Jihohin kasar da kudade domin inganta tsaron su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.