Afrika

Alpha Conde ya sanar da za’a gudanar da zaben shugaban kasar

Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde
Shugaban Guinea Konakry Alpha Conde

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde ya sanar da cewar za’a gudanar da zaben shugaban kasar ranar 18 ga watan Oktoba mai zuwa, watanni bayan sauya kundin tsarin mulkin da zai bashi damar tsayawa wa’adi na uku.

Talla

Kafin dai yiwa kundin tsarin mulkin gyara, shugaban kasa na da damar yin wa’adi biyu ne kacal na shekaru 5-5, amma da yin wannan gyara Conde na da damar fara wani sabon babi.

Hukumar zaben kasar ta bukaci Jam’iyyun siyasa su gabatar da sunayen Yan takarar su nan da gobe alhamis domin tantance su.

Ya zuwa yanzu Conde bai bayyana ko zai tsaya takarar zaben ko kuma zai gabatar da wani ya tsaya a madadin Jam’iyyar sa ba.

Yunkurin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyara ya haifar da kazamar da zanga zanga wadda ta kaiga rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.