Faransa ta hana 'yan kasarta ziyarta wasu yankunan Nijar

Motan ma'aikatan agaji da aka kashe a Nijar
Motan ma'aikatan agaji da aka kashe a Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

Gwamnatin Faransa ta gargadi ‘yan kasarta da su kaucewa ziyartar Jamhuriyar Nijar, face babban birnin kasar Niamey, bayan kissan ‘yan kasar 6 da ‘yan bindiga sukayi a karshen mako.

Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da haka ta shafinta na yanar gizo, cewar kada ‘yan kasar su ziyarci wasu yankunan Nijar din, iyakarsu babban birnin kasar Yamai, sai dai da kwararan dalilai, saboda dalilai na tsaro.

Wannan sabon gargadi na nufin Faransa ta sanya kuduncin jamhuriyar Nijar mai 1 cikin 4 na girman kasar cikin yankuna dake da barazanar tsaro da take kira “Red-Zone” a turance.

Ma’aikatar harkokin wajen na Faransa tace, barazanar tsaro a Nijar ya yi girma, masamman a yankunan dake wajen babban birnin da kuma kan iyakokinta da kasashe makwabta.

Jamhuriyar Nijar dake tsakiyar yankin Sahel, na fama na hare-haren mayaka Boko Haram tun shekarar 2010 ta kan iyakar ta da Nijeriya da Tafkin Chadi, sai kuma ta kan iyakar kasar da Mali daga shekarar 2012.

A ranar Lahadi da ta gabata ‘yan bindiga suka kashe Faransawa ma’aitan agaji 6 a gandun dajin Koure mai nisan kilimita 60 daga babban birnin Yamai, da direbanso da kuma dan rikeya ‘yan Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.