Wasanni-Kwallon kafa

PSG za ta fafata da Atlanta Bergame a Lisbonne

Filin wasa na la Luz, dake Lisbonne a kasar Fotugal
Filin wasa na la Luz, dake Lisbonne a kasar Fotugal FRANCK FIFE / AFP

Yau laraba za a soma wasannin qota final dangane da gasar cin kofin zakarun turai, muna kuma amfani da wannan dama domin sanar da masu sauraren mu cewa tsawon lokacin da za a dauka ana gudanar da wadanan wasanni, ga masu sauraren mu ta zango FM a kasashen Nijar,Kamaru ba za su iya sauraren shirye-shiryen sashen hausa na dare misali karfe 9 na dare agogon Najeriya da Nijar.

Talla

Za a gudanar da akasarin wadanan wasani ba tareda yan kalo ba, yau laraba kungiyar PSG ta Faransa za ta fafatawa da Atlanta Bergame daga Italiya a Lisbonne na kasar Fotugal.

Bangaren PSG ana sa ran dan wasa Kilyan Mbappe ya dawo fage kamar dai yada mai horar da kungiyar Thomas Tuchel ya sheidawa manema labarai, Dan wasan ya gudanar da atisayi a jiya talata akwai alamar zai iya taka gaggarumar rawa a wannan wasa.

Kazalika dan wasan kungiyar dan asalin Brazil Neymar na daga cikin jerryn yan wasan da a kullum yake sa ran taka leda kusa da kylian Mbappe.

Kungiyoyi 8 ne yanzu haka za su kasance a Lisbonne na kasar Fotugal da nufin samun tikitin tsallakawa mataki na gaba a gasar cin kofin zakarun turai.

Kungiyoyin da suka hada da PSG da Lyon daga Faransa,

Bayern Munich da RB Liepzig daga Jamus, Athletico Madrid da Barcalona daga Spain, Atlanta Bergame daga Italiya sai Manchesterd City daga Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.