Rikicin soji da fararen hula a Sudan ta Kudu ya hallaka mutane 127

Fararen hula na guduwa a Sudan ta Kudu
Fararen hula na guduwa a Sudan ta Kudu Justin LYNCH / AFP

Rundunar Sojin Sudan ta Kudu tace mutane 127 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon tashin hankalin da aka samu tsakanin wasu fararen hular dake dauke da makamai da sojoji lokacin da ake kokarin kwance damarar su a garin Tonj dake kasar.

Talla

Manjo Janar Lul Ruai Koang dake Magana da yawun sojin yace rikicin ya barke ne ranar asabar lokacin da ake kokarin karbe makamai daga hannun Yan bindigar.

Janar Lul yace daga cikin mutane 127 da suka mutu, 45 jami’an tsaro ne, yayin da 82 matasa ne dake dauke da makamai.

Jami’in yace wasu sojoji 32 kuma sun samu raunuka.

Rikice rikicen kabilanci ya sa fararen hula da dama na dauke da makamai a cikin kasar, abinda ke kaiga rasa rayuka duk lokacin da aka samu matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI