Najeriya

Tallafin hukumar NFF ga kungiyoyi a Najeriya

Tambarin Hukumar kwallon kafar Najeriya
Tambarin Hukumar kwallon kafar Najeriya completesportsnigeria.com

Hukumar kwallon kafar Najeriya a jiya talata ta bayyana cewa za ta baiwa kungiyoyin kwallon kafar kasar da ma hukumomin dake tafiyar da wasannin kwallon kafa akala milyan biyu na dalla, yi haka na zuwa a matsayin wani tallafi don rage raddadin dakatar da wasanin da aka yi sabili da cutar Covid 19.

Talla

Bayan wata ganawa da Ministan wasani na kasar, kwamitin zartawa na hukumar kwallon kafar Najeriya ya cimma matsaya na ware wadanan kudade ga kungiyoyin ligue ga baki daya.

Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa daga cikin wadanan kudade ta taimaka da milyan daya, kudaden da za su taimaka don dawo da gasar frimiya ta kasa, dubu 500 na dalla tallafi zuwa sashen kwallon kafa na mata,dubu 300 na dalla tallafi daga hukumar kwallon kafa ta Afrika ko CAF, sai dubu 200 daga masoya da masu ra’ayin hukumar kwallon kafar Najeriya NFF

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI