Mutane 4 sun mutu a zanga-zangar adawa da takarar Ouattara

Magoyabayan jam'iyyar RHDP mai mulkin Ivory Coast
Magoyabayan jam'iyyar RHDP mai mulkin Ivory Coast REUTERS/Luc Gnago

Akalla mutane 4 suka mutu sakamakon aranagmar da ta biyo bayan zanga zangar adawa da takarar shugaban kasar cote d’Ivoire Alassane Ouattara wanda ke neman wa’adi na 3 a zaben da za’ayi a watan Oktoba.

Talla

Shaidun gani da ido da majiyoyin tsaro sun ce an kashe mutane 3 a jiya laraba a tsakiyar birnin Daoukro lokacin da aka fafata tsakanin magoya bayan Ouattara da masu goyan bayan abokin adawar sa Henri Konan Bedie.

A yau Alhamis Yan Sanda sun kashe wani matashi mai shekaru 18 a garin Banoua dake da nisan kilomita 50 daga birnin Abidjan lokacin da akayi fito na fito da jami’an tsaro.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun mamaye tashar Yan Sandan Banoua, abinda ya tilastawa jami’an su neman mafaka, kamar yadda wani mazaunin garin Herve Niamkey ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa.

A birnin Abidjan, mutane sun amsa kiran Yan adawa da kungiyoyin fararen hula wajen shiga zanga zangar inda suka tare hanya suna kona tayun mota.

Ouattara mai shekaru 78 ya bayyana aniyar sa ta sake takara a makon jiya, bayan mutuwar Firaministan sa kuma dan takarar Jam’iyar su Amadou Gon Coulibaly.

Ya zuwa yanzu Jam’iyyar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo aa FPI bata bayyana wanda zai tsaya mata takara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI