Wasanni-Kwallon kafa

Bayern Munich ta lallasa Barcelona da ci 8-2

Lionel Messi (FC Barcelona) da Robert Lewandowski (Bayern Munich).
Lionel Messi (FC Barcelona) da Robert Lewandowski (Bayern Munich). REUTERS/Waleed Ali/Michael Dalder

Kungiyar Bayern Munich ta lallasa Barcelona da ci 8-2 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, nasarar da ta bata damar zuwa wasan kusa da na karshe da za’ayi a gasar.

Talla

Muller da Coutinho sun jefa kwallaye bibiyu wa kungiyar Bayern Munich, sai kuma Perisic da Gnabry da Kimmich da kuma Lewandoski da suka jefa kwallo guda guda a luguden da kungiyar ta Jamus ta yiwa Barcelona.

Daga bangaren Barcelona Luis Suarez ya jefa kwallo guda, yayin da Alaba na Bayern yayi kuskuren jefa kwallo guda a gidan su.

Da wannan nasara, Bayern Munich zata kara da kungiyar da ta samu nasara tsakanin Manchester City da Lyon a karawar da za suyi gobe asabar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.