Amurka-Nijar

Wani jirgin yakin Amurka ya yi hatsari a Agadez

Jirgin Amurka marasa matuki a Agadez
Jirgin Amurka marasa matuki a Agadez Daphné BENOIT / AFP

Amurka ta sake yi asarar daya daga cikin jiragen yaki marasa matuki a yankin Tiguirwit dake Agadez arewacin Jamhuriyar Nijar.Idan aka yi tuni a shekara ta 2016 ne kasar Amurka bayan gina wani katafaren filin jiragen saman yaki a garin Agadez rta soma jibge sojojinta da kayakin yaki zuwa yankin.

Talla

Bayanai daga majiyoyin tsaro a kasar sun ce an kashe kudi dalar Amurka Miliyan 100 wajen gina filin jirgin, kuma daya ne daga cikin shirye shirye da suka shafi sha’anin tsaro a Jamhuriyyar Nijar.

Yan lokuta bayan faduwar wannan jirgi marasa matuki a Tiguirwit, kungiyoyi a garin na Agadez sun soma bayyana damuwa tareda yin kira ga hukuma don ganin an kare rayukan farraren hula.

Wannan dai ne karo na uku da ake fuskantar faduwar irin wadanan jirage a Agadez,musaman ranar 29 ga watan fabrairu 2020 a Timia da ranar 23 ga watan Afrilu na 2020 a Aghalin Gharen dake da nisan kilometa 35 da Agadez.

Tun da jimawa ne dai sojojin Amurka suka shiga kasar ta Nijar, inda suke bayar da horo ga sojin kasar, da kuma amfani da jirage marasa matuki samfurin MQ-9 Reaper domin tara bayanan sirri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.