Kamaru

MDD ta koka kan karuwar cin zarafin dan Adam a Kamaru

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric
Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric Reuters

Majalisar dinkin duniya ta hannun kakakinta Stephen Dujarric ta yi tur, da karuwar cin zarafin dan adam a Kamaru, kamar yadda tace bincikenta na baya bayan nan ya nuna.

Talla

Yayin ganawa da manema labarai jiya Juma’a a birnin New York, kakakin majalisar, ya bayyana azaba da kuma kisan gillar da aka yi wa wata mata a garin Muyuka dake kudu maso yammacin Kamaru, a matsayin misali na baya baya.

Tun cikin shekarar 2017, kazamin rikici ya barke tsakanin jami’an tsaro da ‘yan aware a yankunan arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin Kamaru, bayan ikirarin da mayakan ‘yan awaren suka yin a ballewa daga kasar.

Ranar 14 ga watan Fabarairu kadai, rahotanni sun ce akalla fararen hula 23 aka halaka cikinsu harda kananan yara 15 da mata masu ciki biyu, a kauyen Ngarbuh dake arewa maso yammacin kasar ta Kamaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.