Mali-Afrika

shuwagabanin soji Mali da na hukumar leken asirin na haifar da tarnaki

Kwarrarun majalisar dimkin duniya sun zargi shuwagabanin soji da na hukumar leken asirin kasar Mali da haifar da tarnaki ga yinkurin da ake na soma aiki da yarjejeniyar zaman lafiya ta birnin Aljers, duk kuwa da kiraye kirayen da kasashen duniya ke yi, na ganin an magance rikicin dake tsakanin gwamnati da yan tawaye dake arewacin kasar ta Mali.

Shugabannin Afrika ta Yamma 5 sun gaza sasanta rikicin Mali bayan ganawa da shugaba Kieta da kuma 'yan adawa. (26/07/2020)
Shugabannin Afrika ta Yamma 5 sun gaza sasanta rikicin Mali bayan ganawa da shugaba Kieta da kuma 'yan adawa. (26/07/2020) RFI
Talla

A jiya juma’a Kamfanin dillancin labaran AFP dake birnin Paris ya samu rahoton,

Rahoton kwarrarin na Majalisar Dimkin Duniya ya bayyana rashin yarda da kuma rudani tare da tarnaki da shuwagabannin Sojin ke nuna wa wajen hana aiki da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka rattabawa hannu a 2015 tsakanin gwamnatin Bamako da kungiyoyin yan tawayen kasar, da ke zama babbar turbar da za ta kai ga magance matsalolin tsaron da kasar ke fama da su tun shekara ta 2012, bayan daukar makamai da abzinawa yan aware suka yi, da kuma bayyanar mayakan jihadi a yankin arewacin kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI