Afrika ta Kudu

Ramaphosa ya janye dokar haramta sayar da barasa a Afrika ta Kudu

Wani shagon saida barasa a Afrika ta Kudu
Wani shagon saida barasa a Afrika ta Kudu REUTERS/Siphiwe Sibeko

Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya sanar da janye dokar haramta saida barasa da kuma taba Sigari a Daukacin kasar, matakin da y ace zai soma aiki daga ranar litinin.

Talla

Karo na biyu kenan da shugaban Afrika ta Kudun ke haramta saida barasar ya kuma janye dokar, domin hana cinkoson mutane don kare yaduwar annobar coronavirus da ta yiwa kasar Illa fiye da kowace a nahiyar Afrika.

A halin yanzu Afrika ta Kudu ke matsayin ta biyar wajen yawan wadanda suka kamu da cutar corona a duniya, da adadin mutane dubu 583 da 653, daga cikinsu kuma akalla dubu 11 sun halaka.

A cikin watan Afrilun ministan ‘yan sandan Afirka ta Kudu, Bheki Cele, ya ce an samu raguwar aikata miyagun laifuka a cikin manyan biranen kasar sakamakon dokar hana fita da aka kafa don rage yaduwar annobar Coronavirus a watannin baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.