Ghana-Corona

Ghana za ta bude iyakoki da makarantu duk da tsanantar coronavirus

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo. premiumtimesng

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya sanar da cewar gwamnati za ta bude iyakokin kasar ta sama domin zirga zirgar jirage daga ranar 1 ga watan Satumba, yayinda za a bude manyan makarantun kasar daga ranar 24 ga wannan wata.

Talla

Yayin jawabi ga al’ummar kasar shugaban ya ce sun dauki matakin kare lafiyar duk wani matafiyi da kuma dalibi, yayin da cutar korona ta kama mutane 42,532 a cikin kasar, ta kuma kashe wasu 231.

Acewar shugaban ma’aikatar sufurin jiragen sama da hukumar kula da sufurin jiragen sama da kamfanin da ke kula da tashoshin jiragen saman Ghana na aiki tare da ma’aikatar lafiyar kasar da hukumomin ta domin tabbatar da shirin sake bude tashoshin jiragen saman.

Shugaban na Ghana ya ce za su tabbatar yin gwaji ga kowanne fasinja da ya iso kasar domin kare yada cutar ta korona.

Shugaba Nana Akufo-Addo ya kuma bayyana shirin bayar da damar kwaso 'yan kasar da suka makale a ketare don dawo da su gida tare da killace su na akalla makwanni 2 gabanin basu damar shiga cikin jama'a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI