Harin Al-Shebaab ya hallaka mutane 11 a Mogadishu

Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia
Mayakan Al-Shabaab na kasar Somalia RFI-Swahili

Kungiyar Al-Shabaab da dauki alhakin harin wani otel a birnin Mogadishu na kasar Somalia da ya yi sanadiyar hallaka fararen hula 10 da dan sanda daya.

Talla

Kakakin Ma’aikatar watsa labarai na kasar Ismael Mukhtar Omar, yace harin na abubuwa masu fashewa da kuma harbe-harbe da aka kai otel din da ke gabar ruwa, da yammacin jiya Lahadi, ya dauki tsawon sa’o’i na dauki ba dadi tsakanin ‘yan bindiga da jami’an tsaro, kafin nasarar kwace iko da otel din daga hannun mahara.

Omar yace, mutane goma da suka hallaka, sun hada da fararen hula 9 da dan sanda 1, to sai dai yace, an kashe ‘yan bindiga 5.

Babu wani karin haske kan yadda jami’an tsaro sukayi nasarar kashe mayakan da kuma kwanto otel din, wanda abangare daya rahotanni sunce anyi garkuwa da mutane cikin otel sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.