Mali

An jiyo karar harbe-harbe a sansanin sojin Mali dake wajen birnin Bamako

Sojojin kasar Mali.
Sojojin kasar Mali. Michele Cattani/ AFP/ Getty Images

Rahotanni daga Mali sun ce an jiyo karar harbe-harben bindiga a sansanin sojin kasar dake gaf da birnin Bamako, a daidai lokacin da kasar ke fama da rikicin siyasar da ya tayar da hankulan kasashe yammacin Afrika na kungiyar ECOWAS.

Talla

Majiyoyin tsaro da kuma shaidun gani da ido, sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, sojojin Mali ne suka rika harba alburusai cikin iska a sansanin nasu dake yankin Kati mai nisan kilomita 15 daga birnin Bamako.

Wani jami’in tsaro dake sansanin, ya ce ga dukkanin alamu sojojin na harbin iskar ne cikin yanayin dake nuna cewar umarni aka basu, sai dai har yanzu babu karin bayani, kan wanda ya basu umarnin da kuma dalilin yin hakan, abinda ya haifar da tsaro a zukatan jama’a kan fargabar juyin mulki.

A yau talata, ofishin jakadancin Faransa dake kasar ta Mali, ya bukaci jama’a da su zauna a gidajensu, ba tare da yin karin bayani ba.

A halin da ake ciki Mali ta shafe watanni cikin rikicin siyasa, tun bayanda gamayyar ‘yan adawar da ya kunshi ‘yan siyasa da malaman addini suka soma jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnati, tare da shan alwashin tilastawa shugaban kasar Ibrahim Boubacar Kieta yin murabus.

‘Yan adawar dai na tuhumar shugaba Kieta ta gazawa wajen magance matsalolin tsaro na hare-haren ‘yan ta’adda dake ikirarin Jihadi, da kuma rikicin kabilanci, sai kuma matsalar tattalin arziki da kasar ta Mali ta tsinci kanta ciki, musamman tun bayan barkewar annobar coronavirus da ta shafi duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.