Afrika ta Kudu

Kabusai sun shanye sigari a Afrika ta Kudu

Wani mutum da yake busa sigari bayan da Afrika ta Kudus ta sassauta dokar takaita zirga zirga a ranar 18 ga watan Agusta.
Wani mutum da yake busa sigari bayan da Afrika ta Kudus ta sassauta dokar takaita zirga zirga a ranar 18 ga watan Agusta. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Rahotanni daga Afrika ta Kudu sun ce hamshakan kabusai sun karar da ilahirin kararen taba sigarin da suka samu kaiwa gare su, a shagunan dake sassan kasar.

Talla

Mabusa taba sigari a Afrika ta Kudun sun bazama zuwa shagunan sayar da sigari ne, bayan da gwamnati ta janye dokar haramta sayar da tabar da ta shafe watanni 5 tana aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus ta hanyar hana cinkoson jama’a.

Tun a ranar Asabar da ta gabata, 15 ga watan Agustan da muke ciki shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da janye dokar hana sayar da tabar da ma barasa a sassan kasar, matakin da ya soma aiki a ranar Litinin da ta gabata.

Bayanai sun ce fargabar cewa kila gaba gwamnati ta sake maido da dokar ya sanya dubban jama’a tururuwa zuwa shagunan sayar da taba sigarin suka kuma karar da duk wadda suka ci karo da ita.

Yanzu haka dai annobar COVId-19 ta fi yi wa Afrika ta Kudu illa fiye da kowace kasa a Afrika, inda take da adadin sama da mutane dubu 590 da suka kamu da cutar, yayinda annobar ta halaka wasu sama da dubu 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.