Bakonmu a Yau

Kungiyoyin kasa da kasa na yin tir da kifar da gwamnatin Mali

Sauti 03:44
Ibrahim Boubacar Keita, shugaban Mali.
Ibrahim Boubacar Keita, shugaban Mali. Photo: Issouf Sanogo/AFP

Kungiyoyin kasa da kasa na ci gaba da yin tir da kuma Allah wadai da juyin mukin da sojoji suka yi wa shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali, yayin da wani lokaci a  Laraba Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da taron gaggauwa dangane da wannan lamari.Tuni dai sojojin da suka kwaci mulkin suka bayyana aniyarsu ta kafa gwamnatin rikon kwarya, tare da shirya zabubuka don sake mayar da kasar a kan tafarkin dimokuradiyya a nan gaba.A game da wannan lamari ne Abdoulkarim Ibrahim Shikal na zanta da Alkassoum Abdourahman, masani siyasar kasar ta Mali.