Najeriya-Ghana

Najeriya ta sha alwashin daukar mataki kan Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo. Paul Marotta/Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin daukar matakan gaggawa kan yadda hukumomin Ghana ke cin zarafin 'yan kasuwar da suka fito daga kasar, bayan yada wani faifan bidiyo da ke nuna yadda jami’an tsaro ke rufe shagunan 'yan Najeriya a Ghana.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya sanar da haka a madadin gwamnati, matakin da ke zuwa watanni bayan rusa ofishin Jakadancin Najeriyar da ke birnin Accra.

Bidiyon ya nuna wani dan Najeriya da aka rufewa shago, inda yake cewa an bukace shi ya biya Dala miliyan guda a matsayin haraji, yayin da hukumomin Ghana suka musanta ikirarin.

Gwamnatin Ghana ta ce, dokar kasar ta bai wa baki damar fara harkokin kasuwanci ne kawai idan sun zuba jarin da ya kai Dala miliyan guda.

Masu sa ido na bayyana damuwa kan yadda Ghana ta yi karan-tsaye kan dokar ECOWAS wadda ta bai wa mazauna yankin damar tafiye-tafiye da kuma gudanar da harkokinsu ba tare da tsangwama ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.