Mali

Sojin Mali za su gudanar da sabon zaben shugaban kasa

Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali
Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali STRINGER / AFP

Shugabannin sojin da suka yi juyin mulki a Mali sun ce za su shirya zaben da zai mayar da mulki ga fararen hula nan bada dadewa ba.

Talla

Kanar Ismael Wague, mataimakin hafsan sojin saman kasar ya shaida wa al’ummar kasar ta kafar talabijin cewa, kwamitin tsaron kasa ya yanke shawarar daukar matakin juyin mulkin ne domin kare martabar Mali.

Hafsan sojin ya ce Mali ta kama hanyar fadawa cikin rudani da rashin bin doka da oda da kuma rashin tsaro sakamakon rashin jagoranci na gari.

Kanar Wague ya bayyana bacin ransu da abin da ya kira satar dukiyar kasa da almundahana da kama-karya da kuma kisan gillar da ‘yan ta’adda ke yi.

Hafsan ya bukaci kungiyoyin fararen hula da ‘yan siyasa da su hada kai da su domin samar da tsari mai kyau wanda zai kai ga gudanar da karbabben zabe.

Kanar Wague ya bukaci kasashen duniya da na shiya da su taimaka musu domin ceto kasar Mali daga halin da ta samu kanta a ciki, yayin da ya nemi goyan bayan dakarun Majalisar Dinkin Duniya da na Faransa da kungiyar G5 Sahel da na kungiyar kasashen Turai da su taimaka musu a matsayinsu na abokan tafiya.

Sojojin sun bayyana aniyarsu ta mutunta duk yarjeniyoyin da kasar ta amince da su, cikin su har da yarjejeniyar zaman lafiyar Algiers da aka sanya wa hannu a shekarar 2015 tsakanin gwamnatin Mali da kungiyoyin da ke dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.