Sudan

Sudan ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawaye

Abdalla Hamdok Firaministan kasar Sudan
Abdalla Hamdok Firaministan kasar Sudan ASHRAF SHAZLY / AFP

Gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya ta wucin gadi da wata babbar kungiyar 'yan tawayen kasar, wadda za ta kai ga sanya mayakanta cikin rundunar sojin kasar nan da watan Nuwamban shekarar 2023, wanda zai kawo kawo karshen rikicin shekaru da dama.

Talla

Tun a watan Oktoban shakarar da ta gabata, gwamnatin rikon kwaryar, wacce ta karbi mulki bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin Omar al-Bashir a bara, ta fara zaman tattaunawar a makwabciyarta Sudan ta Kudu da manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar guda 4 da har yanzu ba su ajiye makamansu ba.

Wannan Yarjejeniyar na gwamnati da 'yan tawayen Sudan ta SPLM-N) ta shafi jihar Blue Nile da tsaunukan Nuba da ke Kudancin jiyar Kordofan, inda' yan tawayen suka ci gaba da kai farmaki hatta bayan samun ‘yancin Sudan ta Kudu a shekarar 2011.

Kudurorin yarjejeniyar mai shafuka 50, da aka rattaba wa hannu ranar Litinin da ta gabata a Juba babban birnin Sudan ta Kudu, kuma kamfanin dillacin labarai na AFP ya kalla, ya nuna cewa"bangarorin biyu sun cimma matsaya kan shirye-shiryen hadewa da rusa kungiyar da kwance damarar yaki, da kuma shigar da mayaka cikin aikin soji.

Gwamnatin rikon kwaryar Sudan karkashin jagorancin Franminista Abdalla Hamdok, ta bayyana sulhu tsakaninta da ‘yan tawayen SPLM-N a matsayin abu mafi a'ala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI