Zimbabwe

Zimbabwe ta sassauta dokar takaita zirga zirga don ceto kasuwanci

Emmerson Mnangagwa, shugaban Zimbabwe.
Emmerson Mnangagwa, shugaban Zimbabwe. REUTERS/Philimon Bulawayo

Gwamnatin Zimbabwe ta sassauta dokar takaita zirga zirga da a baya ta kafa a daukacin kasar don dakile yaduwar annobar coronavirus, tare da kuma kara yawan sa’o’in dan ta baiwa kasuwanni damar gudanar da hada-hada.

Talla

Bayan kammala taron mako mako na majalisar zartaswar kasar ta Zimbabwe ne, gwamnati ta bayyana sassauta dokar hana fitar dare, inda daga yanzu, a maimakon, hana fita daga karfe 6 na maraice zuwa 6 na safe, dokar za ta soma aiki daga karfe 8 na dare zuwa 4:30 na safe.

Gwamnatin Zimbabwe ta sassauta dokokin takaita zirga-zirgar ce duk da karuwar adadin wadanda suke kamuwa da cutar coronavirus a kasar, inda a yanzu adadin ya kai dubu 5 da 308, yayinda wasu 135 suka mutu.

Wata matsalar da al’ummar kasar ta Zimbabwe ke kokawa a kai kuma ita ce karancin motocin bas na haya, la’akari da cewar tun cikin watan Maris aka dakatar da sufurin kananan motocin tasi, abinda ya tilastawa fasinjoji fama da matsalar tsaikon samun ababen hawa da ke kai su shiga lokacin dokar hana fita a waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.