Mali

'Ni ne jagoran juyin mulki a Mali'

Kanar Assimi Goita
Kanar Assimi Goita France24

Kanar Assimi Goita ya gabatar da kansa a matsayin jagoran sojin da suka yi juyin mulki a Mali, matakin da ya gamu da suka daga kasashen duniya.

Talla

Kungiyar Tarayyar Afrika da Kungiyar Tarayyar Turai da Amurka da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun bukaci sojojin Mali da su gaggauta sakin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da Firaministansa, Boubou Cisse da sauran jiga-jigan gwamnatin da suka kama a yayin juyin mulkin.

Bayan ganawarsa da wasu manyan ma’aikatan gwamnati a birnin Bamako, Kanar Goita ya ce, shi ne shugaban 'Kwatimin Kasa na Ceto Al’umma' wanda ya karbe iko a Mali.

Goita kewaye da sojoji ya shaida wa ‘yan jarudu cewa, Mali na fuskanar tarin matsaloli da suka hada da rikicin siyasa, kuma ba za a sake samun wata kafar tafka kura-kurai ba a cewarsa.

Mukarrabansa sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, Goita mai shekaru 40 da doriya, ya taba jagorantar wata runduna ta musamman da ke tsakiyar Mali wadda rikicin mayakan jihadi ya daidaita a tsawon shekaru biyar.

Kazalika majiyoyi da dama sun tabbatar wa AFP cewa, lallai babu shakka, Goita shi ne ya jagoranci shirin kifar da gwamnatin Keita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.