Afrika-Coronavirus

An samu raguwar masu kamuwa da Coronavirus a nahiyar Afrika

Zuwa tsakar ranar yau Alhamis dai nahiyar ta Afrika na da jumullar mutum miliyan 1 da dubu 147 da 369 wadanda coronavirus ta kama.
Zuwa tsakar ranar yau Alhamis dai nahiyar ta Afrika na da jumullar mutum miliyan 1 da dubu 147 da 369 wadanda coronavirus ta kama. Arsene Mpiana / AFP

Hukumar hana yaduwar cuta ta nahiyar Afrika ''Africa CDC'' ta sanar da samun raguwar sabbin kamuwa da coronavirus a kasashen nahiyar, dai dai lokacin da hukumar ke shirin fara wani gwajin allurar rigakafin cutar rukunin farko wanda kasashen nahiyar 7 za su amfana ciki har da Liberia Saliyo Zambia Zimbabwe Najeriya da kuma Maroko.

Talla

Cikin bayanan shugaban hukumar Dr John Nkengasong yayin wani taron manema labarai, ya ce daga makon jiya nahiyar na samun adadin mutum dubu 10 da 300 ne sabbin kamuwa kowacce rana, sabanin dubu 11 da ta ke samu a baya, wanda ke nuna gagarumar nasara a yakin da ake da yaduwar cutar.

Dr John ya bayyana cewa samun raguwar mutanen da ke kamuwa da cutar kowacce rana ya nuna yiwuwar samun nasarar kammala yakar cutar cikin sauri.

Acewarsa duk ya ke annobar coronavirus babbar barazana ce ga bangaren lafiya na duniya baki daya, amma samun nasara a yaki da cutar duk kankantarta abar alfahari ce.

Zuwa tsakar ranar yau Alhamis dai nahiyar ta Afrika na da jumullar mutum miliyan 1 da dubu 147 da 369 wadanda coronavirus ta kama adadin da kusan rabinsa ke Afrika ta kudu wadda ke matsayin ta 5 a jerin kasashe masu yawan wadanda ke dauke da cutar a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.