Afrika-Ecowas

Shugabanin Ecowas zasu tura tawaga zuwa Mali

Taron Shugabanin kasashen Ecowas
Taron Shugabanin kasashen Ecowas Cdéao/Reuters

Shugabannin kungiyar ECOWAS zasu tura tawaga zuwa Mali domin ganawa da sojojin da suka yi juyin mulki da zummar ganin sun koma bariki domin mayar da doka da oda a kasar ta Mali.

Talla

Shugaban Jamhuriyar Nijar dake jagorancin kungiyar Mahamadou Issufou ya bayyana haka bayan taron da suka gudanar yau ta bidiyo inda suka yi nazari kan halin da ake ciki a kasar ta Mali.

Shugaba Issufou yace tawagar da zai jagoranta zuwa Mali zata shaidawa sojojin karara cewar lokacin amfani da karfin soji wajen kwace mulki ya wuce a Afirka.

ECOWAS ta bukaci mayar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita karagar mulki ba tare da bata lokaci ba.

Taron shugabanin Ecowas dangane da batun Mali

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.