Mali

Sojin Mali na shirin nada shugaban rikon kwarya

Mai magana da yawun Sojin Mali,  Ismael Wagué, a jawabinsa gaban taron manema labarai.
Mai magana da yawun Sojin Mali, Ismael Wagué, a jawabinsa gaban taron manema labarai. AFP/Annie Risemberg

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun bayyana shirin nada shugaban rikon kwarya da zai jagoranci kasar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zabe.

Talla

Mai magana da yawun sojin, Ismael Wague ya shaidawa tashar France 24 cewar za su kafa Majalisar rikon kwarya wadda za ta kunshi shugaban kasa na soji ko farar hula da zai jagorance ta.

Jami’in ya ce suna cigaba da tintibar bangarori da dama da suka hada da kungiyoyin fararen hula da ‘yan adawa da wadanda aka kifar da gwamnatin su domin kafa majalisar rikon kwaryar.

Wague ya ce ba zai iya bayyana lokacin da za su mika mulki ba, amma dai a shirye su ke su shirya zabe domin mayar da mulki ga fararen hula.

Kakakin sojin ya yi watsi da zargin cewar su suka tilastawa shugaba Ibrahim Bounacar Keita bayyana murabus din sa, inda ya ke cewa ya sauka ne sakamakon kashin kan sa saboda ganin yadda jama’ar kasar ke shan wahala.

Dangane da makomar shugaban kuwa, Wague ya ce bangaren shari’a ne kawai zai yanke hukunci akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.