Morocco

'Yan cirani da dama sun jikkata a arangamarsu da jami'an tsaron Morocco

Wasu 'yan ciranin Afrika a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai.
Wasu 'yan ciranin Afrika a kokarinsu na tsallakawa nahiyar Turai. REUTERS/Ismail Zitouny

Akalla mutum guda ya rasa ransa yayinda wasu 8 kuma suka jikkata sakamakon arangama tsakanin wasu ‘yan ciranin Afrika da jami’an tsaro a kokarinsu na tsallakawa Spain ta tsibirin Melilla da ke matsayin mashiga Turai daga Morocco a yau Alhamis.

Talla

Dan ciranin guda wanda ba a kai ga gano suna ko kuma kasar da ya fito ba, bayanai sun nuna cewa ya fado ne daga katanga mai tsayin kafa 16 ko da dai wani bincike na daban ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon bugun zuciya.

Majiyar ‘yansandan Morocco ta ce 8 cikin ‘yan ciranin sun samu raunukan da suke karbar kulawar gaggawa a asibiti.

Cikin sanarwar da kasar ta fitar, ta ce 30 cikin ‘yan cirani 300 da suka yi yunkurin shiga tsibirin na Melilla da tsallakawa nahiyar Turai ta Spain su ne suka iya shige matakan tsaron da ta gindaya.

A cewar anarwar gwamnatin Moroccon wannan ne karon farko da wani ayarin ‘yan cirani mai yawa ya yi yunkurin shiga tsibirin na Melilla iyaka ta kasa daya tilo tsakanin nahiyar Afrika da nahiyar Turai.

Tun bayan matakan kulle da kasashe suka dauka don dakile yaduwar coronavirus ne aka samu karancin ‘yan ciranin da ke kokarin tsallakawa nahiyar Turai.

Cikin watanni 7 na farkon shekarar da ta gabata ‘yan cirani dubu 3 da 136 suka tsallaka tsbirin na Melilla daga Morocco don neman ingantacciyar rayuwa a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.