Mali

Dubun dubatar magoya bayan 'yan adawa na gangamin nasara a Mali

Dubun dubatar magoya bayan ‘yan adawa ne suka gudanar da taron gangami yau juma’a a birnin Bamako, domin bayyana farin cikinsu a game da abin da suka kira nasarar da al’ummar kasar suka samu wajen kawo karshen mulkin Ibrahim Boubacar Keita.

Wasu magoya bayan 'yan adawa a Mali.
Wasu magoya bayan 'yan adawa a Mali. ANNIE RISEMBERG / AFP
Talla

Dubban magoya bayan ‘yan adawar sun taru ne a dandalin ‘yancin kai da ke tsakiyar birnin Bamako, dandalin da suka share tsawon makonni suna gudanar da gangami neman ganin Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga karagar mulki.

Da farko an gudanar da sallar juma’a ne a wannan dandali kamar yadda suka saba, kafin daga bisani a fara gabatar da jawabai don nuna murnar faduwar gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita wanda sojoji suka kifar a ranar talatar da gabata.

A lokacin gangami, magoya bayan ‘yan adawar sun rika furta kalaman nuna jinjina ga sojoji, yayin da wasu daga cikinsu ke kira ga sojojin da su yi kokarin ganin an saki jagoran ‘yan adawa Soumaila Cisse, wanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi tun cikin watan maris d ya gabata.

Yanzu haka dai kasar ta Mali ta shiga a cikin wani sabon babi, bayan da sojoji suka kaddamar da bore, tare da cafke hambararren shugaban da firaministansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI