Libya

Haftar ya sanar da tsagaita wuta

Abdel Fattah al-Sisi na Masar,tareda rakiyar Khalifa Haftar da Shugaban majalisar Libya Aguila Saleh
Abdel Fattah al-Sisi na Masar,tareda rakiyar Khalifa Haftar da Shugaban majalisar Libya Aguila Saleh Présidence égyptienne/AFP

Bayan share sama da shekara daya ana gwabza fada tsakanin dakarun janar Haftar da mayakan gwamnatin hadin kan kasar Libya,bangaren jagoran yan tawayen kasar a yau juma'a,Shugaban mayakan  ya sanar da tsagaita wuta tareda kiran babban zabe a kasar ta Libya da ta fada cikin wani yanayi na rashin tabbas tun bayan mutuwar Mohammar Ghadafi.

Talla

Kasashe da suka jima suna kai da kawo don ganin an warware rikicin na Libya suka yaba yan lokuta da samun labarin tsagaita wuta daga bangaren janar Haftar.

kazzalika Majalisar Dimkin Duniya ta bayyana farin cikin samun labarin  da safiyar yau juma'a.

Rikicin Libya ya haddasa asarar rayuka da dama,da kuma tilastaw da dama daga cikin yan kasar da baki  barin matsugunin su ba tareda shiri ba.

Ana sa ran ,shugaban gwamnatin  hadin kan kasar Fayez al-Sarraj ya gabatar da jawabi don nuna amincewar gwamnatin da yake jagoranta biyo bayan wannan sanarwa daga bangaren yan tawaye Khalifa Haftar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.