Wasanni

Sevilla zata kara da Inter Milan a gasar Europa

Sauti 10:32
Romelu Lukaku dan wasan Inter Milan
Romelu Lukaku dan wasan Inter Milan Pool via Reuters/Martin Meissner TPX IMAGES OF THE DAY

A yau juma’a Inter Milan zata fafata da Sevilla a gasar cin kofin Europa a birnin Cologne na kasar Jamus da misalin karfe 7 agogon GMT, takwas kenan agogon Najerita da Nijar.Sevilla za ta yi kokarin kare martabar kungiyoyin kasar Spain, yayinda Inter Milan a nata geffen za ta nemi sake dawo da sunan Italiya sahun kasashe dake girmama kwallon kafa a Duniya.

Talla

Masu nazari a duniyar kwallon kafa na dada nuna cewa wannan dai somin tabi ne daga cikin wasannin da za su gudana a wannan mako ,domin ranar lahadi, Bayern Munich za ta ketse reni da PSG a Lisbon na kasar Fotugal dangane da gasar cin kofin zakarun turai.

Karawar yau tsakanin yan wasan Sevilla a karkashin mai horar da su Julien Lopetegui da Inter Milan a karkashin Cochi Antonio Conte za ta kasance wasar da jama’a za su raja’a, kasancewa kungiyar Inter Milan da yan wasa da suka hada da Romeo Lukaku,Lautaro Martinez da suke taka tamola a Inter Milan kowanen su na da kwallaye 54 a kakar wasa ta bana za su haskawa domin sake dawo da murna a zukatan ma’abuta kwallon kafar Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.