Afrika-Ecowas

Shekara daya bayan rufe kan iyakokin Najeriya da Nijar,Benin,Kamaru da Chadi

Kan iyaka ta Seme Krake  tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin
Kan iyaka ta Seme Krake tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Ranar 20 ga watan Agusta aka cika shekara daya da Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya bayar da umurni na rufe kan iyakokin kasar da Nijar,Jamhuriyar Benin,Kamaru da Chadi.

Talla

Ga baki daya wannan matsallar ta shafi daukacin yan kasuwa da kamfanoni dake gudanar da harakokin sun a yau da na kullum a yankin Ecowas,musaman kasashen dake raba iyaka da Najeriya.

Ta bangaren diflomasiya,ana ci gaba da tattaunawa don warware matsallar kamar yada karamin jakadan Jamhuriyar Benin a Najeriya Muktari Ali Daura ya sanar,a ko da yaushe suna cikin tattaunawa da hukumomin Najeriya.

Karamin jakadan na bayyana cewa za a samar da mafita nan da bada jimawa ba.

Matakin da ga baki daya ya haifar da koma baya ga lamuran tattalin arzikin wasu kasashen ,kamar dai yada zaku ji ta bakin, Moussa Salau daya daga cikin masu gudanar da harakokin su na yau da na kullum tsakanin Najeriya da Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.