Amurka-Mali

Amurka ta katse tallafin sojin da take baiwa Mali

Wani sojan Amurka, yayin sa ido kan horon da suke baiwa sojojin kasar Mali garin Gao. 13/11/2006
Wani sojan Amurka, yayin sa ido kan horon da suke baiwa sojojin kasar Mali garin Gao. 13/11/2006 REUTERS/Luc Gnago

Amurka ta sanar da katse duk wani tallafi da take baiwa Mali ta fuskar soji, a matsayin martaninta kan juyin mulkin da sojin kasar ta Mali suka yi da ya kawo karshen shugabancin Ibrahim Boubacar Kieta.

Talla

Yayin ganawa da Manema labarai, Jakadan Amurka a yankin sahel J. Peter Pham yace kai tsaye sun dakatar da baiwa sojin Mali horo da kuma tallafin makamai, har zuwa lokacin da hali yayi.

Matakin na Amurka na zuwa yayin da dubban ‘yan kasar ta Mali suka gudanar da gangamin nuna farin cikin kawo karshen gwamnatin shugaba Kieta a birnin Bamako a Juma’ar nan da ta gabata.

Dubban magoya bayan ‘yan adawar sun taru ne a dandalin ‘yancin kai da ke tsakiyar birnin Bamako, dandalin da suka share tsawon makonni suna gudanar da gangami neman ganin Ibrahim Boubacar Keita ya sauka daga karagar mulki.

Zuwa wannan lokacin dai babu duriyar hambararren shugaban na Mali tun bayan sanarwar yin murabus da kuma ruse gwamnatinsa da yayi a ranar Talata, 18 ga watan Agustan da muke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.