Ebola-Congo

Annobar Ebola ta sake barkewa a Jamhuriyar Congo

Wasu jami'an lafiya a Jamhuriyar Congo.
Wasu jami'an lafiya a Jamhuriyar Congo. John WESSELS/AFP/File

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadin cewa al’ummar Jamhuriyar Congo na fuskantar barazanar sake barkewar annobar Ebola, bayanda alkalumma suka nuna cewar akalla mutane 100 sun kamu da cutar a kasa ta watanni 3.

Talla

Wannan ta sanya hukumar ta WHO gargadin, gami da kokawa kan cewar hukumomin lafiyar Jamhuriyar ta Congo basu da isassun kudaden fuskantar cutar.

Karo na 11 kenan da annobar ta Ebola ke barkewa a kasar ta Congo, tun bayan bullarta a shekarar 1976, kuma yanzu haka cutar ta bazu zuwa akalla lardunan kasar 11 daga cikin 17, inda ta halaka mutane 43 a baya bayan nan.

Ana yada cutar ce ta hanyoyi da dama da suka hada da ruwan jiki da jini ko bahaya da fistari ko kuma daga jikin gawar mutumin da Ebolar ta kashe.

Cutar ta sake bulla ne a daidai lokacin da kasar ta Congo ke da mutane fiye da dubu 8 da suka kamu da sabuwar cutar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.