Najeriya

Bangarorin dake rikici a kudancin kaduna sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya

Jami'an tsaro na suturi a wasu yankunan Kaduna
Jami'an tsaro na suturi a wasu yankunan Kaduna REUTERS/Stringer

Kabilun Atyap da Fulani da Hausawa dake rikici a Zangon Kataf dake Jihar Kadunan Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin su bayan kwashe dogon lokaci basa ga maciji da juna.Wannan ya biyo bayan taron zaman lafiyar da aka kira inda bangarorin suka yi Allah wadai da kashe kashen da aka samu da lalata dukiyoyi, inda suka yafewa juna da zummar hada kai da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Talla

Bangarorin sun yaba rawar da gwamnatin ke takawa wajen girke Karin jami’an tsaro, yayin da suka yabawa matasa daga bangarorin dake rikicin saboda amincewa su cire da shingen da aka girke akan hanyoyin dake yankin.

Taron sasantawar da aka gudanar a karkashin jagorancin Basaraken Yankin, Agwatyap, Dominic Gambo Yahya tare da tsohon hafsan sojin sama mai ritaya, Air Marshall Stephen Shekari ya kunshi wakilan al’ummomi guda 3 dake yankin.

Sanarwar bayan taron da wakilan bangarorin 3 suka rattabawa hannu ta bukaci kaucewa daukar doka da oda da gabatar da duk wani korafi ga hukumomi, yayin da taron yayi Allah wadai da hana mutane zirga zirga ko walwala a yankin.

Taron ya bukaci hukumomin Jihar da su sanya hannu wajen taimakawa mutanen da suka gudu daga yankin saboda tsira da rayukan su komawa inda suke da kuma kafa kwamitin zaman lafiya tsakanin kabilun 3, wato Atyap da Hausa da Fulani da kuma wakilan matasa da zasu dinga tattauna matsalolin da ake samu lokaci zuwa lokaci domin tabbatar da zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.