Afrika

Kasashen Afrika sun samu nasarar dakushe kaifin annobar coronavirus

John Nkengasong, shugaban hukumar yaki da yaduwar cutuka ta nahiyar Afrika CDC. 11/3/2020.
John Nkengasong, shugaban hukumar yaki da yaduwar cutuka ta nahiyar Afrika CDC. 11/3/2020. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo

Cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Afrika CDC, tace hukumomin kasashen nahiyar sun soma samun nasarar dakile annobar coronavirus, biyo bayan daukar matakan tilastawa jama’a sanya takunkuman rufe baki da hanci da kuma rage cinkoson jama’a.

Talla

Da fari dai sannu a hankali annobar ta coronavirus ta soma yaduwa a Afrika, kafin daga bisani karfin yaduwar cutar yayi karuwar bazata musamman a Afrika ta Kudu, kasar da ta kunshi sama da rabin mutane miliyan 1 da dubu 100 da suka kamu da cutar ta corona a nahiyar Afrika.

Sai dai yayin karin bayani a karshen mako, shugaban cibiyar yaki da yaduwar cutuka ta Afrika CDC John Nkengasong, sabbin alkalumma sun nuna cewar yawan mutanen dake kamuwa da cutar COVID-19 ya ragu a tsawon makwanni 2 da suka gabata.

Yanzu haka dai yawan mutanen da annobar ta kashe a nahiyar Afrika ya kai dubu 26 da 622, daga cikin mutane miliyan 1 da dubu 148 da 455 da suka kamu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.