Cote d'Ivoire

Shugaba Ouattara ya amince da tsayawa takarar zaben shugaban kasar

Magoya bayan Shugaba Alassane Dramane Ouattara a filin wasa na Abidjan
Magoya bayan Shugaba Alassane Dramane Ouattara a filin wasa na Abidjan Issouf SANOGO / AFP

Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya amince da bukatar Jam’iyyar sa na tsayawa takarar zaben shugaban kasar da za’ayi a watan Oktoba domin yin wa’adi na 3.

Talla

A wani gagarumin taron da aka yi a filin wasa mai suna Stade Felix Houphouet Boigny na Abidjan, Ouattara ya godewa magoya bayan Jam’iyyar sa da suka amince ya sake takara domin cigaba da jagorancin kasar.

Waje dama cikin kasar yan Adawa na ci gaba da bayyana rashin amincewar su da sake tsayawa takarar Shugaban kasar.

Magoya bayan shugaban kasar na kalon sa a matsayin  mutumen da ya taka gaggarumar rawa don sake dawo da zaman lahiya,ya kuma farfado da tattalin arzikin ta ga baki daya.

Takarar shugaban mai shekaru 78 ta haifar da zanga zanga da kuma arangama da jami’an tsaro, abinda yayi sanadiyar rasa rayuka a wasu yankunan kasar ta Cote D'Ivoire.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.