Afrika

Shugabannin Afirka da aka kora daga karagar mulki

Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Mamadou Tandja
Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar Mamadou Tandja AFP/Boureima Hama

A farkon wannan mako ne sojoji a kasar Mali suka gudanar da juyin mulki inda suka kawar da shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita daga karagar mulki.Keita shine shugaban kasa na 15 da aka tilastawa sauka daga karagar mulki a Afirka a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Talla

A ranar 18 ga watan Fabarairun shekarar 2010, sojoji a Jamhuriyar Nijar sun kawar da shugaban kasa Mamadou Tandja bayan ya sauya kundin tsarin mulkin kasar domin samun damar yin wa’adi na uku.

A ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2011, juyin juya hali ya kifar da gwamnatin Firaminista Zine El Abidine Ben Ali, wanda ya gudu ya bar kasar bayan ya kwashe shekaru 23 a karagar mulki.

A ranar 11 ga watan Fabarairun shekarar 2011 zanga zanga ta tilastawa shugaba Hosni Mubarak na Masar sauka daga kujerar sa bayan ya kwashe shekaru 30 yana mulki, abinda ya baiwa sojoji damar hawa karagar shugabanci.

A ranar 11 ga watan Afrilun shekarar 2011, jami’an tsaro suka kama shugaban Cote d’Ivoire Laurent Gbagbo bayan tashin hankalin da ya biyo zaben shugaban kasar wanda aka bayyana Alasassne Ouattara a matsayin wanda ya lashe.

A ranar 20 ga watan Oktobar shekarar 2011 yan tawayen Libya da taimakon kungiyar tsaro ta NATO suka kashe shugaban kasar Libya Moammar Ghadafi wanda ya kwashe kusan shekaru 42 a karagar mulki.

A ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2012, sojoji suka yi bore a Mali inda suka kama shugaban kasa Amadou Toumane Toure.

A ranar 12 ga watan Afrilun shekarar 2012 sojoji suka kama shugaban kasar Guinea Bissau Raimundo Pereira da tsohon Firaminista Carlos Gomes Junior sakamakon takaddamar zaben shugaban kasa.

A ranar 24 ga watan Maris na shekarar 2013, yan tawayen kungiyar Seleka suka tilastawa shugaba Francois Bozize tserewa daga karagar mulki, inda suka nada shugaban su Michel Djotodia a karaga, yayin da shima a ranar 10 ga watan Janairun shekarar 2014 ya sauka daga mulki sakamakon matsin lambar kasashen duniya.

A ranar 31 ga watan Oktobar shekarar 2014, sojoji suka tilastawa shugaba Blaise Compaore da ya kwashe shekaru 27 a karagar mulki tserewa ya bar kasar, yayin da kasa da shekara guda aka tilastawa wanda ya gaje shi, shugaban rikon kwarya Michel Kafando sauka daga mukamin, kafin daga bisani aka mayar da shi.

A ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2017 Yahya Jammeh ya fice ya bar Gambia bayan ya sha kashi a zaben shugaban kasar, sakamakon nasarar da Adama Barrow ya samu.

A ranar 21 ga watan Nuwambar shekarar 2017, shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe da ya kwashe shekaru 37 a karagar mulki ya sauka daga mukamin sa, bayan da Majalisar dokoki ta fara mahawarar tsige shi, yayin da tsohon mataimakin sa Emmerson Mnangagwa ya gaje shi.

A ranar 14 ga watan Fabarairun shekarar 2018, shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya sauka daga karagar mulki sakamakon yunkurin tsige shi saboda zargin cin hanci da rashawa, abinda ya baiwa mataimakin sa kuma shugaban Jam’iyyar ANC Cyril Ramaphosa damar zama shugaban kasa.

A ranar 2 ga watan Afrilun shekarar 2019, shugaban Algeria Abdelaziz Bouteflika da ya kwashe shekaru 20 a karagar mulki ya sauka daga mukamin sa sakamakon zanga zangar tsadar rayuwa da kuma bukatar sa ta neman wa’adi na biyar.

A ranar 11 ga watan Afrilun bana sojoji sun kifar da gwamnatin shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir sakamakon zanga zangar da ak kwashe watanni 4 anayi a kasar, matakin da ya bada damar kafa gwamnatin rikon kwarya da ta kunshi soji da fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.