Afrika-Ecowas

Tawagar ECOWAS ta gana da sojojin da suka yi juyin mulki

Tawagar Ecowas a Bamako yan lokuta bayan sauka daga cikin jirgi
Tawagar Ecowas a Bamako yan lokuta bayan sauka daga cikin jirgi ANNIE RISEMBERG / AFP

Tawagar kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta isa Mali domin ganawa da sojojin da suka kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita dan ganin an gaggauta mayar da mulki ga fararen hular kasar.

Talla

Ana sa ran tawagar wadda ke karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta gana da hambararren shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita dake tsare a barkin soji da kuma shugabannin sojin.

Shugabannin ECOWAS sun ki amincewa da kwace ikon a taron gaggawa da suka gudanar ranar alhamis, matsayin da ya samu goyan bayan Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar kasashen Afirka ta AU da kuma kasashen Faransa da Amurka.

Sai dai ga alama Yan adawar Mali sun amince da juyin mulkin kamar yadda suka bayyana a taron gangamin da suka gudanar jiya a Bamako, inda suka bayyana aniyar su ta aiki tare da sojojin domin mayar da Mali turbar dimokiradiya.

Tuni kungiyar ECOWAS ta hannu shugaban ta Mahamadou Issofou ta sanar da takunkumi kan kasar ta Mali da kuma wasu daga cikin jami’an sojin da suka karbe iko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.