Najeriya

Ya dace kowa ya mallaki bindiga a Najeriya - Gwamna

Bindiga
Bindiga Claire Bargelès - RFI

Gwamnan Jihar Benue dake Najeriya Samuel Ortom ya sake kira ga gwamnatin kasar da ta baiwa jama’a damar mallakar bindiga domin kare kan su daga hare hare ganin yadda matsalar tsaro ke cigaba da fadada.Ortom yace matakin ya zama wajibi inda ya bukaci jama’ar Najeriya da su farka daga barci domin daukar mataki kada su bari yan bindiga su gama da su.

Talla

Gwamnan yace yaji mahawarar da mutane keyi saboda ya bukaci a bar jama’a su mallaki bindigogi domin kare kan su, inda suke cewa hakan zai jefa kasa cikin rudani, amma kuma babu wanda yake magana kan Yan bindigar da suka mallaki bindigogi kirar AK-47 kuma suke garkuwa da mutane da yiwa mata fyade da lalata kauyuka da garuruwa.

Ortom yace menene dalilin da aka gaza wajen karbe makaman dake hannun wadannan Yan bindigar, kuma ya zuwa yanzu guda nawa aka kama daga cikin su.

Gwamnan yace yayin da gwamnatin tarayya taki cewa komai dangane da kiran da yayi, sai ga shi an kama wasu masu garkuwa da mutane da suka mallaki bindiga kirar AK-47.

Ortom ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki shawarar sa da matukar muhimmanci saboda ko a Amurka gwamnati na baiwa jama’a lasisin mallakar bindigogi domin kare kan su.

Gwamnan yace har yanzu yana kan bakar sa wajen wannan kira na ganin gwamnati ta amince da bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.