Najeriya

Dubban mutane suka tarbi tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi 2

Dubban mutane suka tarbi Tsohon Sarkin Kano a Kaduna
Dubban mutane suka tarbi Tsohon Sarkin Kano a Kaduna Daily Trust

Dubban Mutane ne suka yi gangami a Kaduna dake Najeriya domin tarbar tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II wanda ya isa birnin daga Lagos inda ya koma tun bayan warware rawanin sa da Gwamnan Kano Abdullahi Uma Ganduje yayi.

Talla

Rahotanni sun ce manyan titunan Kaduna sun cika makil sakamakon jerin gwanon motocin da suka dauko tsohon Sarkin daga tashar jiragen Kaduna zuwa fadar gwamnatin jihar inda ya gana da Gwamna Nasir Ahmad El Rufai.

Jami’an tsaro sun yiwa tawagar rakiya wanda ke dauke da tarin motoci da baburan dake dauke da daruruwan magoya bayan tsohon Sarkin wanda ya sauka a Kaduna da misalin karfe 10.30 na safiyar yau daga wani jirgin sama mai zaman kan sa.

Bayanai sun ce tsohon Sarkin zai gana da tarin magoya bayan sa da suka yi asubanci daga Kano zuwa Kaduna, bayan ganawa da abokin sa Gwamna El Rufai.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II daga Sarautar Kano ranar 9 ga watan Maris na wannan shekarar saboda abinda ya kira rashin biyayya ga hukumomi.

Bayan sauke shi daga Sarautar Kano, Gwamnan Kaduna Nasir El Rufai ya nada Muhammadu Sanusi shugaban gudanarwar Jami’ar jihar Kaduna da kuma mataimakin shugaban Hukumar zuba jari ta Jihar Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.