Mali

Harin bam ya halaka sojojin Mali 4

Wasu dakarun sojin Mali yayin sintiri a garin Gao.
Wasu dakarun sojin Mali yayin sintiri a garin Gao. Reuters

Sojin Mali 4 sun rasa rayukan su yayinda guda ya jikkata a jiya asabar, bayanda motar su ta taka nakiya a lokacin da suke sintiri a yankin tsakiyar kasar.

Talla

Mutuwar dakarun na Mali a yankin Koro mai iyaka da Burkina Faso na zuwa ne kasa da mako guda bayan juyin mulkin da sojojin kasar suka yi na kawo karshen shugabancin Ibrahim Boubacar Keita da ya sanar da yin murabus gami da rusa gwamnatinsa a ranar Talata, 18 ga Agustan da muke.

A ranar Alhamis sojin na Mali suka baiwa tawagar Jami’an kare hakkin dan Adam na majalisar dinkin duniya damar ganawa hambararren shugaban kasar dake tsare tare da wasu manyan makarrabansa 17.

Sojin sun sha alwashin gaggauta shirya zabuka don sake mikawa farar hula gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.