Najeriya

An kashe mutane 415 a Najeriya a watan Yuli - Rahoto

Wasu da suka tserewa rikici daga yankunan su
Wasu da suka tserewa rikici daga yankunan su Dailytimes

Wani bincike ya nuna cewar akalla mutane 415 aka kashe a Najeriya a watan Yulin da ya gabata sakamakon hare hare da kuma tashin hankalin da ake cigaba da samu a cikin kasar.

Talla

Wata kungiya da ta kira kan ta ‘Nigeria Mourn’ tace an fi samun kashe kashen dake da nasaba da hare haren Yan bindiga da rikicin book haram da kuma barayin shanu ne a Jihohin Kaduna da Borno da Katsina.

Alkaluman kungiyar sun ce daga cikin Jihohi 21 da aka kashe mutane 415, Jihar Kaduna ke sahun gaba da mutane 139, sai Barno mai 113, Katsina na da 80, Kogi 17, Nasarawa 13, Taraba 10, Benue 9 sai kuma Ebonyi mai 8.

Sauran sun hada da Zamfara mai mutane 7, Plateau 5, Edo da Akwa Ibom da Lagos na da bibiyu, sai kuma Jihohin Oyo da Imo da Rivers da Cross Rivers da Ogun da Bayelsa da Delta da kuma Kebbi dake da guda-guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.